An-Nisaa 4:95
النساءلَّا يَسْتَوِى ٱلْقَـٰعِدُونَ مِنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ غَيْرُ أُو۟لِى ٱلضَّرَرِ وَٱلْمُجَـٰهِدُونَ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ بِأَمْوَٰلِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ ۚ فَضَّلَ ٱللَّهُ ٱلْمُجَـٰهِدِينَ بِأَمْوَٰلِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ عَلَى ٱلْقَـٰعِدِينَ دَرَجَةً ۚ وَكُلًّا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلْحُسْنَىٰ ۚ وَفَضَّلَ ٱللَّهُ ٱلْمُجَـٰهِدِينَ عَلَى ٱلْقَـٰعِدِينَ أَجْرًا عَظِيمًا
Mãsu zama[1] daga barin yãƙi daga mũminai, wasun ma'abũta larũra da mãsu jihãdi a cikin hanyar Allah da dũkiyõyinsu da rãyukansu, bã su zama daidai. Allah Yã fĩfĩta mãsu jihãdi da dũkiyoyinsu da rãyukansu a kan mãsu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Yã yi musu alkawari da abu mai kyau.[2] Kuma Allah yã fĩfĩta mãsu jihãdi a kan mãsu zama da lãda mai girma.
[1] Falalar mãsu jihãdi a kan waɗanda ba su jihãdi daga cikin muminai. Faɗar falalar tana ƙarfafa zukãta ga yin jihãdi domin tsaron addini da rãyukan mãsu rauni da dũkiyarsu.
[2] Aljanna.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net