Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 83

An-Nisaa 4:83

النساء

وَإِذَا جَآءَهُمْ أَمْرٌ مِّنَ ٱلْأَمْنِ أَوِ ٱلْخَوْفِ أَذَاعُوا۟ بِهِۦ ۖ وَلَوْ رَدُّوهُ إِلَى ٱلرَّسُولِ وَإِلَىٰٓ أُو۟لِى ٱلْأَمْرِ مِنْهُمْ لَعَلِمَهُ ٱلَّذِينَ يَسْتَنۢبِطُونَهُۥ مِنْهُمْ ۗ وَلَوْلَا فَضْلُ ٱللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُۥ لَٱتَّبَعْتُمُ ٱلشَّيْطَـٰنَ إِلَّا قَلِيلًا

Ma’ana

Kuma idan wani al'amari[1] daga aminci ko tsõro ya je musu, sai su wãtsa shi. Dã sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abũta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, zã su san shi. Kuma bã dõmin falalar Allah bã a kanku da rahamar Sa, haƙĩƙa, dã kun bi Shaiɗan fãce kaɗan.

[1] Umurnin al'umma da cewa idan sun ga wani al'amari daba su san kansa ba kõ kuwa idan wani abu na ban tsõro ya auku, to, haram ne su yi ta bãrãrarsa domin su firgitar da mutãne. Abin da yake wãjibi a kansu sa'an nan, shi ne su kai rahõtonsa ga shugabanni mãsu sanyãwa a bincika asan yadda abin yake, da kuma yadda zã a yi mãganinsa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net