Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 64

An-Nisaa 4:64

النساء

وَمَآ أَرْسَلْنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذْنِ ٱللَّهِ ۚ وَلَوْ أَنَّهُمْ إِذ ظَّلَمُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ جَآءُوكَ فَٱسْتَغْفَرُوا۟ ٱللَّهَ وَٱسْتَغْفَرَ لَهُمُ ٱلرَّسُولُ لَوَجَدُوا۟ ٱللَّهَ تَوَّابًا رَّحِيمًا

Ma’ana

Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã'a da izinin Allah. Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu,[1] sun zo maka sa'an nan suka nẽmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.

[1] Wanda ya ƙi hukuncin Allah, ya yi laifi biyu, domin sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wannan ya nũna rashin ĩmãninsa da Allah da Manzon Sa. Saboda haka ne ãyã mai bin wannan ta ce Musulmi bã su da ĩmãni sai sun yarda da Hukuncin Allah ga kome daga al'amurransu, kuma su yarda da hukuncinsa, bã da jin wani ƙunci a cikin zukatansu ba.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net