Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 43

An-Nisaa 4:43

النساء

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَقْرَبُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنتُمْ سُكَـٰرَىٰ حَتَّىٰ تَعْلَمُوا۟ مَا تَقُولُونَ وَلَا جُنُبًا إِلَّا عَابِرِى سَبِيلٍ حَتَّىٰ تَغْتَسِلُوا۟ ۚ وَإِن كُنتُم مَّرْضَىٰٓ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَآءَ أَحَدٌ مِّنكُم مِّنَ ٱلْغَآئِطِ أَوْ لَـٰمَسْتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَلَمْ تَجِدُوا۟ مَآءً فَتَيَمَّمُوا۟ صَعِيدًا طَيِّبًا فَٱمْسَحُوا۟ بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَفُوًّا غَفُورًا

Ma’ana

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye[1], sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna mãsu janaba, fãce mai ƙẽtare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kãshi, kõ kuwa kun shãfi mãtã ba ku sãmi ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shãfa ga fuskokinku da hannuwanku.[2] Lalle ne Allah Yã kasance Mai yãfẽwa Mai gãfara.

[1] A lokacin ba a hana shan giya ba. Sa'an nan aka hana ta da ayar Suratul Ma'idah ta 90. Mai janaba kuma ba ya yin salla kuma ba ya shiga masallaci sai ya yi wanka ko taimama, sai dai yana iya shiga da niyyar wucewa daga ƙõfa zuwa ga wata, ko kuwa ya shiga ya ɗebo ruwa ya fita. Ana yin taimama saboda rashin ruwa haƙiƙatan, ko ma'anan, kamar mai rashin lafiya. Shafar mace na karya alwala, amma ba ya sabbaba wanka idan an yi shafar da niyyar jin dãɗi ko kuma an sami jin dãɗin ba da nufi ba. Mai shafar da wanda aka shafa duka ɗaya suke.
[2] Wãtau ku yi taimama sabõda rashin ruwa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net