Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 157

An-Nisaa 4:157

النساء

وَقَوْلِهِمْ إِنَّا قَتَلْنَا ٱلْمَسِيحَ عِيسَى ٱبْنَ مَرْيَمَ رَسُولَ ٱللَّهِ وَمَا قَتَلُوهُ وَمَا صَلَبُوهُ وَلَـٰكِن شُبِّهَ لَهُمْ ۚ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ ٱخْتَلَفُوا۟ فِيهِ لَفِى شَكٍّ مِّنْهُ ۚ مَا لَهُم بِهِۦ مِنْ عِلْمٍ إِلَّا ٱتِّبَاعَ ٱلظَّنِّ ۚ وَمَا قَتَلُوهُ يَقِينًۢا

Ma’ana

Da faɗarsu:[1] "Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsã ɗan Maryama Manzon Allah," alhãli kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kẽre shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a garẽ su. Lalle ne waɗanda sauka sãɓã wa jũna a cikin sha'aninsa lalle ne, sunã shakka daga gare, shi, bã da wani ilmi fãce bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni.

[1] Faɗarsu ta izgili watau suna cewa: "Mun kashe ĩsã ɗan Maryama wanda yake da'awar shi Manzon Allah ne." Asalin maganar Yahũdu suka karkatar da Dãwũda sarkin Dimashƙa, da cewa ga wani mutum nan yana ɓãta ƙasa da aƙĩdar mutãne a Baitil Maƙdis sabõda haka ya bãyar da õda ga hãkimansa a Baitil Maƙdis da a kashe ĩsã sai suka tafi suka tsare shi a cikin gida shi da sahabbansa, watau Hawãriyawa. ĩsã ya rõki waninsu da yarda da kisa a kan sakamakon Aljanna. Sai ƙaraminsu ya yarda, Allah Ya sanya masa sifar ĩsã, a bãyan haka Ya ɗauke ĩsã. Shi kuma aka kashe shi matsayin ĩsã. Daga nan,Yahũdu suna zaton sun kashe shi, kuma waɗanda suka halarci ƙissar, suka sãɓã wa jũna wajen sifar ĩsã da cewa Shi ne Allah, ko ɗan Allah, ko ɗayan uku, ko manzon Allah, kamar yadda ya gabãta a cikin Baƙara.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net