Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 150

An-Nisaa 4:150

النساء

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكْفُرُونَ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيُرِيدُونَ أَن يُفَرِّقُوا۟ بَيْنَ ٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ وَيَقُولُونَ نُؤْمِنُ بِبَعْضٍ وَنَكْفُرُ بِبَعْضٍ وَيُرِيدُونَ أَن يَتَّخِذُوا۟ بَيْنَ ذَٰلِكَ سَبِيلًا

Ma’ana

Lalle ne, waɗanda uke kãfirta da Allah da ManzonSa kuma sunã nufin su rarrabe[1] a tsakãnin Allah da manzanninSa, kuma sunã cẽwa: "Munã ĩmãni da sãshe, kuma munã kãfirta da sãshe." Kuma sunã nufin su riƙi hanya a tsakãnin wannan.

[1] Rarrabewa tsakãnin Allah da ManzanninSa, shi ne mutum ya ce ga misãli, "Na yarda Allah gaskiya ne, zan yi duka abin da yake mai kyau saboda Shi, amma bãbu ruwãna da wani Annabi kõ wani manzõ," ko kuma ya ce ai duk addĩnai ɗaya ne, ana nufin Allah da su, sai mutum ya bi abin da ya ga dama. Duka irin waɗannan maganganu bã su da kyau, kãfirci ne.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net