An-Nisaa 4:134
النساءمَّن كَانَ يُرِيدُ ثَوَابَ ٱلدُّنْيَا فَعِندَ ٱللَّهِ ثَوَابُ ٱلدُّنْيَا وَٱلْـَٔاخِرَةِ ۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعًۢا بَصِيرًا
Wanda ya kasance[1] Yanã nufin sakamakon dũniya, to, a wurin Allah sakamakon dũniya da Lãhira yake. Kuma Allah Yã kasance Mai ji, Mai gani.
[1] Wannan shi ne ƙarshen wasiyya ga Yahũdu da Nasãra da kuma Musulmi kuma ma'anar wasiyya ĩta ce Allah Yã yi umurni da ku yi Masa ɗã'a amma bã domin Yana neman wani abu daga gare ku ba, domin bã zã ku ƙãra Masa mulki ba, dõmin shi ne da sammai da ƙasa da abin da ke tsakaninsu kũ kuma kuna cikinsu. Saboda haka neman ɗã'ar nan domin amfanin kanku ne.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net