Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 127

An-Nisaa 4:127

النساء

وَيَسْتَفْتُونَكَ فِى ٱلنِّسَآءِ ۖ قُلِ ٱللَّهُ يُفْتِيكُمْ فِيهِنَّ وَمَا يُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فِى ٱلْكِتَـٰبِ فِى يَتَـٰمَى ٱلنِّسَآءِ ٱلَّـٰتِى لَا تُؤْتُونَهُنَّ مَا كُتِبَ لَهُنَّ وَتَرْغَبُونَ أَن تَنكِحُوهُنَّ وَٱلْمُسْتَضْعَفِينَ مِنَ ٱلْوِلْدَٰنِ وَأَن تَقُومُوا۟ لِلْيَتَـٰمَىٰ بِٱلْقِسْطِ ۚ وَمَا تَفْعَلُوا۟ مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِهِۦ عَلِيمًا

Ma’ana

Sunã yi maka fatawa a cikin sha'anin mãtã. Ka ce: "Allah Yanã bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantãwa a kanku a cikin Littãfi, a cikin sha'anin marãyun mãtã waɗanda ba ku bã su abin da aka rubũta musu[1] (na gãdo) ba, kuma kunã kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yãra, da sha'anin tsayuwarku ga marãyu da ãdalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yã kasance Masani a gare shi."

[1] A cikin jahiliyya ba su bai wa yãra da mãtã gãdo. Musulunci ya sõke wannan al'ãda da ãyar gãdo, ãyã ta 11. Kuma idan akwai wata marainiya ga hannun wani tana da dũkiya, sai ya jefa mata mayafinsa domin ya hana ta auren wani namiji. Shi kuma ko ya aure ta ko kuma ya bar ta bãbu aure har ta mutu, su yi gãdon ta.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net