Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 109

An-Nisaa 4:109

النساء

هَـٰٓأَنتُمْ هَـٰٓؤُلَآءِ جَـٰدَلْتُمْ عَنْهُمْ فِى ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا فَمَن يُجَـٰدِلُ ٱللَّهَ عَنْهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ أَم مَّن يَكُونُ عَلَيْهِمْ وَكِيلًا

Ma’ana

Gã ku, yã waɗannan[1]! Kun yi jidãli, dõmin tunkuɗe musu (kunya) a cikin rãyuwar dũniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Rãnar ¡iyãma? Ko kuwa wãne ne zai kasance wakĩli a kansu?

[1] Wannan yana nũna aikin lauya (Lawyer) dõmin ya taimaki marasa gaskiya sabõda ya kuɓuta harãmun ne, har dai idan zã a mayar da laifi ga wani barrantacce ko kuwa za a karɓe hakkin mai hakki a bai wa wanda bai cancanta da shi ba. Amma wakĩlin sharĩ'a yana halatta idan bai zama dõmin ɓõye gaskiya ba. Wakĩlai irin na zãmanin nan mãsu sanã'a da wannan, sũ ne karnukan dũniya na farautar haram dõmin su sha jini.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net