Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 105

An-Nisaa 4:105

النساء

إِنَّآ أَنزَلْنَآ إِلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ بِٱلْحَقِّ لِتَحْكُمَ بَيْنَ ٱلنَّاسِ بِمَآ أَرَىٰكَ ٱللَّهُ ۚ وَلَا تَكُن لِّلْخَآئِنِينَ خَصِيمًا

Ma’ana

Lalle ne, Mũ, Mun saukar,[1] zuwa gare ka, Littãfi da gaskiya, dõmin ka yi hukunci a tsakãnin mutãne da abin da Allah Ya nũna maka, kuma kada ka kasance mai husũma dõmin mãsu yaudara.

[1] Gudãnar da hukunci a cikin mahakama, kada mai shari'a ya taimaki kowane sãshe, duk yadda suke a gare shi, sai ya ɗauke su daidai a gabansa, kamar yadda ya auku a gaban Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi. Wani mutum Musulmi ana ce masa Mat'ama bn Ubairak ya yi sãtar sulke ya ɓõye shi a wurin wani Bayahũde. A lõkacin da aka gãne sulken a wurin Bayahũden, sai Mat'ama ya yi masa ƙazafi da sãtarsa, shi kuma yayi rantsuwa cewa bã shi ne ya sãtã ba. Kuma mutãnensa suka rõƙi Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, dõmin ya yi musu jãyayya yakuɓutar da mat'ama, Annabi kuwa bai yarda ba. Kamar yadda ãyõyin nan suka bayyana, domin ya zama abin kõyi. Wannan kuma ya nũna cewa, ga gudanar da sharĩ'a Annabi yana yin ijtihãdi gwargwadon abin da ya bayyana daga hujjoji ya yi hukunci, kamar wajen shãwara a wurin yãki. Ya zama abin kõyi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net