Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 4 · Aya ta 1

An-Nisaa 4:1

النساء

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُوا۟ رَبَّكُمُ ٱلَّذِى خَلَقَكُم مِّن نَّفْسٍ وَٰحِدَةٍ وَخَلَقَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالًا كَثِيرًا وَنِسَآءً ۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ٱلَّذِى تَسَآءَلُونَ بِهِۦ وَٱلْأَرْحَامَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَيْكُمْ رَقِيبًا

Ma’ana

Ya ku mutãne! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza mãsu yawa da mãtã. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke rõƙon jũna da (sũnan), shi, da kuma zumunta.[1] Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne.

[1] Bin Allah Wanda Ya halitta ku, kira ga tabbatar da tauhidin Ulũhiyya ne da Rubũbiyya. Fitar mutãne daga asali guda, wanda bãbu wani surki a cikinsa yana wajabtar da girman jinsin mutum, kõwane iri ne, kowane launi, kuma kõwace halitta yake ɗauke da ita.Tsõron Allah da tsaronSa a kan mutãne yana wajabtar da tsayãwa a cikin haddõdin sharĩ'arSa. Tsõron zumunta ko rantsuwa da ita yana wajabtar da tausayi da rahama a kan halittar Allah na kusa da na nesa. Hadĩsi ya nũna ba a yin rantsuwa da wanin Allah sabõda haka ma'anar aya itace, 'Ku ji tsõron Allah ku tsare mahaifa da zumunta!'.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Nisaa

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net