Saad 38:35
صقَالَ رَبِّ ٱغْفِرْ لِى وَهَبْ لِى مُلْكًا لَّا يَنۢبَغِى لِأَحَدٍ مِّنۢ بَعْدِىٓ ۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْوَهَّابُ
Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna.[1] Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
[1] Yã yi wannan addu'a dõmin kada wani ya yi alfahari da sarauta a bãyansa, ya halaka kuma ya halakar da wani. Sarauta ita ce asalin girman kai da alfahari. Bã ka ganin wanda ya shiga wajan sarki, dõmin ya gaishe shi, idan ya fito daga gare shi, sai ya ɗõra yin tãƙama dõmin abin da zuciyarsa ta ɗebo daga girman kan sarkin da alfaharinsa?.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net