Saad 38:24
صقَالَ لَقَدْ ظَلَمَكَ بِسُؤَالِ نَعْجَتِكَ إِلَىٰ نِعَاجِهِۦ ۖ وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ ٱلْخُلَطَآءِ لَيَبْغِى بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَقَلِيلٌ مَّا هُمْ ۗ وَظَنَّ دَاوُۥدُ أَنَّمَا فَتَنَّـٰهُ فَٱسْتَغْفَرَ رَبَّهُۥ وَخَرَّ رَاكِعًا وَأَنَابَ ۩
(Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce[1] ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara, kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah.
[1] Dãwũda ya yi hukunci da zãlunci ga wanda ya yi ƙãra, sabõda abin da ya rufe shi na ƙin zãluntar mai rauni wanda Allah Ya hana. Nauyin wani laifi ya rufe shi daga tunãwa da wani laifi, watau yin hukunci tun binciken shari'a bai cika ba, sabõda iya maganar wani abõkin ƙãra. Wannan shĩ ne fitinar da ta same shi kawai kuma a kanta ya yi nadãma, kuma a kanta ne Allah Ya yi masa gargaɗin kada ya bi son rai mai sanya Fushi kõ yarda ga abin da bai cancanci haka ba. Yarda da wata ƙissar mãtar Uriya wadda Yahũdãwa ke sanyãwa, a nan, kãfirci ne ga Musulmi, dõmin ta kõre ismar Annabãwa, kuma ba ta dãce da lafazin Alƙur'ãni ba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net