Saba 34:23
سبإوَلَا تَنفَعُ ٱلشَّفَـٰعَةُ عِندَهُۥٓ إِلَّا لِمَنْ أَذِنَ لَهُۥ ۚ حَتَّىٰٓ إِذَا فُزِّعَ عَن قُلُوبِهِمْ قَالُوا۟ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ ۖ قَالُوا۟ ٱلْحَقَّ ۖ وَهُوَ ٱلْعَلِىُّ ٱلْكَبِيرُ
"Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurin Sa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye[1] tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma,"
[1] Bãbu wanda ya san lõkacin bãyar da izni ga yin ceto kõ wanda zã a bai wa iznin ya yi, kõ a yi masa, Sabõda haka mutãne a Lãhira na cikin tsõro har a lõkacin da aka koranye tsõron ta hanyar bãyar da izni ga ceto babba ga Annabi Muhammadu, sai mũminai su yi farin ciki su dinga tambayar jũna da cewa, "Menene Ubangijinku Ya ce?" waɗansu su ce, "Yã faɗi gaskiya' Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma.".
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net