Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 33 · Aya ta 69

Al-Ahzaab 33:69

الأحزاب

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَكُونُوا۟ كَٱلَّذِينَ ءَاذَوْا۟ مُوسَىٰ فَبَرَّأَهُ ٱللَّهُ مِمَّا قَالُوا۟ ۚ وَكَانَ عِندَ ٱللَّهِ وَجِيهًا

Ma’ana

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci[1] Mũsã sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah.

[1] Kada ku cũci Muhammadu da ƙazafĩ kõ mũguwar magana kamar yadda Yahũdu suka yi ƙazafi ga Mũsã da neman wata kãruwa ta ce yã neme ta da zina kõ kuma da cewa shi mai gwaiwa ne, sai Allah Ya tsare Mũsã daga ƙazafin' kuma Ya sanya wani dũtse, ya gudu da tufãfinsa daga wurin wanka har suka gan Shi mai cikakkiyar halitta ne, bãbu naƙasa game da shi. Allah Yã barrantar da shi daga dukan aibi. Haka Yake barrantar da Muhammadu ga mai son ya sa masa aibi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Ahzaab

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net