Al-Ahzaab 33:60
الأحزابلَّئِن لَّمْ يَنتَهِ ٱلْمُنَـٰفِقُونَ وَٱلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌ وَٱلْمُرْجِفُونَ فِى ٱلْمَدِينَةِ لَنُغْرِيَنَّكَ بِهِمْ ثُمَّ لَا يُجَاوِرُونَكَ فِيهَآ إِلَّا قَلِيلًا
Lalle, idan munãfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukãtansu, da mãsu tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba (daga hãlãyensu),[1] lalle, zã Mu shũshũta ka a gare su, sa'an nan bã zã su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, fãce kaɗan.
[1] Munãfukai da Shaiɗãnu da mãsu tsegumi bãbu abin da ke hana su mugun hãlinsu sai tsanani da tsõrõ.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net