Al-Ahzaab 33:51
الأحزابتُرْجِى مَن تَشَآءُ مِنْهُنَّ وَتُـْٔوِىٓ إِلَيْكَ مَن تَشَآءُ ۖ وَمَنِ ٱبْتَغَيْتَ مِمَّنْ عَزَلْتَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكَ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰٓ أَن تَقَرَّ أَعْيُنُهُنَّ وَلَا يَحْزَنَّ وَيَرْضَيْنَ بِمَآ ءَاتَيْتَهُنَّ كُلُّهُنَّ ۚ وَٱللَّهُ يَعْلَمُ مَا فِى قُلُوبِكُمْ ۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَلِيمًا
Kanã iya jinkirtar da[1] wadda ka ga dãmã daga gare su, kuma kanã tãro wadda kake so zuwa gare ka. Kuma wadda ka nẽma daga waɗanda ka nĩsantar, to, bãbu laifi agare ka. Wannan yã fi kusantar da sanyaya idãnunsu, kuma bã zã su yi baƙin ciki ba, kuma su yarda da abin da ka bã su, sũ duka. Kuma Allah Yanã sane da abin da yake a cikin zukãtanku. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai haƙuri.
[1] Rabon kwãna ga mãtan Annabi, ba sharĩ'a ba ce a kan hususiyyarsa, sabõda yawan nauyin da yake ɗauke da Shi na isar da Manzancin Allah.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net