Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 33 · Aya ta 26

Al-Ahzaab 33:26

الأحزاب

وَأَنزَلَ ٱلَّذِينَ ظَـٰهَرُوهُم مِّنْ أَهْلِ ٱلْكِتَـٰبِ مِن صَيَاصِيهِمْ وَقَذَفَ فِى قُلُوبِهِمُ ٱلرُّعْبَ فَرِيقًا تَقْتُلُونَ وَتَأْسِرُونَ فَرِيقًا

Ma’ana

Kuma Ya saukar [1]da waɗannan da suka taimake su daga mazõwa Littãfi, daga birãnensu, kuma Ya jẽfa tsõro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kunã kashẽwa, kuma kunã kãma wata ƙungiyar.

[1] Sa'an nan kuma Musulmi suka tsare Yahũdun Bani Ƙuraiza, a cikin birninsu har suka sallama kansu ga hukuncin sa'ad bn Mu'azu wanda ya hukunta a kashe wanda ya balaga daga cikinsu, kuma a bautar da mãtã da yãra. Aka yi musu hakanan, aka zartar da hukuncinsa a kansu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Ahzaab

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net