Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 33 · Aya ta 13

Al-Ahzaab 33:13

الأحزاب

وَإِذْ قَالَت طَّآئِفَةٌ مِّنْهُمْ يَـٰٓأَهْلَ يَثْرِبَ لَا مُقَامَ لَكُمْ فَٱرْجِعُوا۟ ۚ وَيَسْتَـْٔذِنُ فَرِيقٌ مِّنْهُمُ ٱلنَّبِىَّ يَقُولُونَ إِنَّ بُيُوتَنَا عَوْرَةٌ وَمَا هِىَ بِعَوْرَةٍ ۖ إِن يُرِيدُونَ إِلَّا فِرَارًا

Ma’ana

Kuma a lõkacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce, "Ya mutãnen Yasriba![1] Bã ku da wani matsayi, sabõda haka ku kõma." Kuma wata ƙungiya daga gare su na nẽman izni ga Annabi sunãcẽwa, "Lalle gidãjenmu kuranye suke," alhãli kuwa bã kuranye suke ba, bã su da nufin kome fãce gudu.

[1] Sun kõma ga sũnan Madĩnan a zãmanin Jãhiliyya sunã izgili da cewa ba su yarda da sãbon sũnan ba na Madĩna, fãce Yasriba, sũnanta da suka sani na asali.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Ahzaab

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net