Luqman 31:27
لقمانوَلَوْ أَنَّمَا فِى ٱلْأَرْضِ مِن شَجَرَةٍ أَقْلَـٰمٌ وَٱلْبَحْرُ يَمُدُّهُۥ مِنۢ بَعْدِهِۦ سَبْعَةُ أَبْحُرٍ مَّا نَفِدَتْ كَلِمَـٰتُ ٱللَّهِ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Kuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su ƙãre ba.[1] Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
[1] Wannan bayãni ne ga yawan ilmin Allah, watau yanã nũnawa mutãne cewa su yi aiki da ilmin da Ya bã su, mai amfãni zuwa gare su, kada su wuce shi zuwa neman wani ilmi daga wani abu, su bar Allah, su halaka a kan wani ilmi da bai umurce su da su yi aiki da shi ba. Ilmin da Ya bã su a cikin Alƙur'ãni shi ne sharĩ'a wãtau hanya mai kai su ga Aljanna. Sauran hanyõyi ɓata ne.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net