Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 31 · Aya ta 15

Luqman 31:15

لقمان

وَإِن جَـٰهَدَاكَ عَلَىٰٓ أَن تُشْرِكَ بِى مَا لَيْسَ لَكَ بِهِۦ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا ۖ وَصَاحِبْهُمَا فِى ٱلدُّنْيَا مَعْرُوفًا ۖ وَٱتَّبِعْ سَبِيلَ مَنْ أَنَابَ إِلَىَّ ۚ ثُمَّ إِلَىَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

Ma’ana

"Kuma idan mahaifanka suka tsananta[1] maka ga ka yi shirki game da Ni, ga abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'a. Kuma ka abũce su a cikin dũniya gwargwadon sharĩ'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa gare Ni, sa'an nan zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

[1] A bãyan haƙƙin Allah sai haƙƙin iyãye. Sabõda haka ba zã a yi ɗã'a ga iyãye ba ga abin da ya sãɓãwa Allah.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Luqman

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net