Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 30 · Aya ta 2

Ar-Room 30:2

الروم

غُلِبَتِ ٱلرُّومُ

Ma’ana

An rinjãyi Rũmawa.[1]

[1] Rũmãwa Kiristoci ne mãsu aiki da littãfi, sunã faɗa da Fãrisãwa mãsu bautã wa wutã. Fãrisawa suka rinjãyi Rumãwa, sabõda haka Ƙuraishãwa suka ji dãɗi sabõda alfãnun cewa zã su rinjãyi Musulmi idan sun yi faɗa. A bãyan saukar surar, sai Musulmi suka yi farin ciki sabõda alfãnun cewa sũ kuma zã su rinjãyi Ƙuraishãwa. Wannan ya sanya Abũbakar ya yi ƙuri'a da Ubaiyu bn Halaf a kan rãƙuma gõma a cikin shekaru uku. Sai Annabi ya ce wa Abũbakar ya ƙãra rãkuma da ajãli zuwa shekaru tara. A bãyan shekaru bakwai sai Rũmawa suka ci nasara a kan Fãrisãwa, kuma wannan ya yi daidai da Badar,watau rãnar da Musulmi suka ci nasara a kan Ƙuraishãwa. Abũbakar ya ci rãƙumansa daga magãdan Ubaiyu. Amma sai ya yi sadaka da su da umurnin Annabi, dõmin Allah Yã hana Musulmi su yi cãca a lõkacin.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Ar-Room

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net