Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 3 · Aya ta 96

Aal-i-Imraan 3:96

آل عمران

إِنَّ أَوَّلَ بَيْتٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِى بِبَكَّةَ مُبَارَكًا وَهُدًى لِّلْعَـٰلَمِينَ

Ma’ana

Kuma lalle ne, ¦aki na farko[1] da aka aza dõmin mutãne, haƙĩƙa, shi ne wanda ke Bakka[2] mai albarka kuma shiriya ga tãlikai.

[1] Ɗãkunan Allah a cikin ƙasa dõmin mutãne su yi ibãda zuwa gare su biyu ne; Ka'aba a Makka da Baitil Muƙaddas. An gina Ka'aba a gabaninsa da shekara arba'in. Dãkin Bakka kuwa Ibrãhĩma ne ya gina shi alhãli Yahũdu da Nasãra sunã cewa kan addininsa suke. Dã sunã faɗar gaskiya dã sun kõma a gare shi gabã ɗaya.
[2] Ana ce wa Makka Bakka.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Aal-i-Imraan

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net