Aal-i-Imraan 3:61
آل عمرانفَمَنْ حَآجَّكَ فِيهِ مِنۢ بَعْدِ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا۟ نَدْعُ أَبْنَآءَنَا وَأَبْنَآءَكُمْ وَنِسَآءَنَا وَنِسَآءَكُمْ وَأَنفُسَنَا وَأَنفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَل لَّعْنَتَ ٱللَّهِ عَلَى ٱلْكَـٰذِبِينَ
To, wanda ya yi musu[1] da kai a cikinsa, a bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirãyi, 'yã'yanmu da 'yã'yanku da mãtan mu da mãtanku da kanmu da kanku sa'an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa'an nan kuma mu sanya la'anar, Allah a kan maƙaryata."
[1] Wanda ya yi hujjacewa da Annabi a kan sha'anin Ĩsã; kamar Nasãran Najrãn, sun tafi dõmin su yi jãyayya da Annabi. Ya kira su zuwa ga mubãhala, suka ce: sai sun yi shãwara, suka ce wa jũnansu: "Kun san gaskiya mutumin nan Annabi ne. Ku bar ra'ayinku na mubãhala, dõmin wani Annabi bai taɓa yin ta tãre da wasu mutãne ba, fãce sun halaka." Bãyan haka suka iske Annabi yã fito shi da Hasan da Husaini da Fãtima da Ali, kuma ya ce musu: "ldan na yi addu'a ku ce, Ãmin." Sai suka ƙi mubahãlar, suka yi sulhu akan jizya.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net