Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 3 · Aya ta 199

Aal-i-Imraan 3:199

آل عمران

وَإِنَّ مِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَـٰبِ لَمَن يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيْهِمْ خَـٰشِعِينَ لِلَّهِ لَا يَشْتَرُونَ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ ثَمَنًا قَلِيلًا ۗ أُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلْحِسَابِ

Ma’ana

Kuma lalle ne daga Mutãnen Littãfi[1] haƙĩƙa akwai wanda yake yin ĩmãnĩ da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, sunã mãsu tawãlu'i ga Allah, bã su sayen tamani kaɗan da ãyõyin Allah. Waɗannan suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugãwar sakamako da yawa ne.

[1] A cikin Mutãnen Littãfi akwai mutãnen ƙwarai na kirki waɗanda hãsada ba ta hana su bin gaskiya ba. Sun sifantu da sifõfin kamãla; watau ba dukkansu ne miyagu ba. Akwai na ƙwarai a cikinsu kamar yadda hãli yake a kõwane tãron mutãne.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Aal-i-Imraan

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net