Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 3 · Aya ta 179

Aal-i-Imraan 3:179

آل عمران

مَّا كَانَ ٱللَّهُ لِيَذَرَ ٱلْمُؤْمِنِينَ عَلَىٰ مَآ أَنتُمْ عَلَيْهِ حَتَّىٰ يَمِيزَ ٱلْخَبِيثَ مِنَ ٱلطَّيِّبِ ۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُطْلِعَكُمْ عَلَى ٱلْغَيْبِ وَلَـٰكِنَّ ٱللَّهَ يَجْتَبِى مِن رُّسُلِهِۦ مَن يَشَآءُ ۖ فَـَٔامِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦ ۚ وَإِن تُؤْمِنُوا۟ وَتَتَّقُوا۟ فَلَكُمْ أَجْرٌ عَظِيمٌ

Ma’ana

Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai[1] Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba.[2] Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa.[3] Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma.

[1] Watau Allah bã zai bar mutãne su ce: 'Mun yi ĩmãni, da bãki kawai ba,' sai Yã jarraba su Ya fitar da mũminan ƙwarai daga munãfukai. Sabõda haka Ya sanya rãnaiku kamar rãnar Uhdu wadda Allah Ya jarrabi mũminai da ĩta har haƙurinsu da ɗã'arsu suka bayyana, kuma munãfukai suka bayyana.
[2] Allah bai sanar da gaibi ga mutãne waɗanda ba Annabãwa ba, sabõda haka bã ku iya sanin ĩmãnin mutum ko rashin ĩmãninsa, sai da alãma ta wani aikĩ ko magana wadda take da ita za a iya yin hukunci da kãfirci ko ĩmãnĩ ga mutum.
[3] Allah Yã zãɓi wanda Ya so daga manzanninSa, watau Yã zaɓi Annabi Muhammadu da ƙãrin daraja a kan sauran Annabãwa da falalarsa. Wannan ne mafificin yabo a gare shi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Aal-i-Imraan

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net