Aal-i-Imraan 3:172
آل عمرانٱلَّذِينَ ٱسْتَجَابُوا۟ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِ مِنۢ بَعْدِ مَآ أَصَابَهُمُ ٱلْقَرْحُ ۚ لِلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ مِنْهُمْ وَٱتَّقَوْا۟ أَجْرٌ عَظِيمٌ
Waɗanda suka karɓa[1] kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki ya sãme su. Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata[2] yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa.
[1] Bayan kõmawar Musulmi daga Uhdu da miyãkun da suka sãme su, sai Annabi ya umurce su da fita a bãyan kãfirai, dõmin kada su yi tunãnin kõmãwa. Sai suka fita bãyansu, aka dãce kuwa Abu Sufyãna ya umurci mutãnensa da kõmawa Madĩna dõmin su tumɓuke Musulmi. An yi Uhdu ta farko ran Asabat, sa'an nan suka fita a bãyansu a rãnar Lahadi, suka riske su a Hamra'al Asad. Sai aka yi tawãfuƙi (yarjejeniya) tsakanin Annabi da Abu Sufyãna a kan a bar yãƙi a lõkacin, sai shekara mai zuwa, a haɗu a Badar. Allah Ya yabi Musulmi, da suka karɓa wannan kira, a cikin miyãkũ. Haka duka mai karɓawa irinsu, yã shiga a cikin irin wannan yabo har ya zuwa tãshin Ƙiyãma.
[2] Kyautata yi shi ne tsarkake aiki dõmin Allah watau ihsani kõ ihlasi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net