Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 3 · Aya ta 169

Aal-i-Imraan 3:169

آل عمران

وَلَا تَحْسَبَنَّ ٱلَّذِينَ قُتِلُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمْوَٰتًۢا ۚ بَلْ أَحْيَآءٌ عِندَ رَبِّهِمْ يُرْزَقُونَ

Ma’ana

Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu[1]. Ana ciyar da su.

[1] A cikin Hadisi an ruwaito cewa, Annabi yã ce Allah Yanã sanya rũhinsu a cikin cikkunan tsuntsãye mãsu kõren launi, sunã tafiya da su a cikin Aljanna sunã ci daga 'ya'yan itãcenta da rãna, sa'an nan su kõma zuwa ga wasu fitillu waɗanda aka rãtaye a cikin inuwar Al'arshi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Aal-i-Imraan

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net