Aal-i-Imraan 3:167
آل عمرانوَلِيَعْلَمَ ٱلَّذِينَ نَافَقُوا۟ ۚ وَقِيلَ لَهُمْ تَعَالَوْا۟ قَـٰتِلُوا۟ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ أَوِ ٱدْفَعُوا۟ ۖ قَالُوا۟ لَوْ نَعْلَمُ قِتَالًا لَّٱتَّبَعْنَـٰكُمْ ۗ هُمْ لِلْكُفْرِ يَوْمَئِذٍ أَقْرَبُ مِنْهُمْ لِلْإِيمَـٰنِ ۚ يَقُولُونَ بِأَفْوَٰهِهِم مَّا لَيْسَ فِى قُلُوبِهِمْ ۗ وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يَكْتُمُونَ
Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe.[1]" Suka ce: "Dã mun san (yadda ake) yãƙi dã mun bĩ ku." Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa.
[1] Ku tunkuɗe mana maƙiyã da duhunku, kõ dã ba ku yi yãƙi ba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net