Aal-i-Imraan 3:165
آل عمرانأَوَلَمَّآ أَصَـٰبَتْكُم مُّصِيبَةٌ قَدْ أَصَبْتُم مِّثْلَيْهَا قُلْتُمْ أَنَّىٰ هَـٰذَا ۖ قُلْ هُوَ مِنْ عِندِ أَنفُسِكُمْ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ
Shin kuma a lõkacin[1] da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rãyukanku[2] yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne.
[1] Duk masĩfar da ta sãme ku, tõ, ku ne kuka jãwo wa kanku ita da wani laifi na sãɓãwa umurnin Allah. Kuma kãmin masĩfa guda ta sãme ku, to, alheri biyu sun sãme ku.
[2] Kowace irin masĩfa ta sãmi mutum, to, shĩ ne ya yi sababinta a kansa. Kuma yã kamata ya yi bincike ya gãne sababin, a inda ya jãhilce shi. Kuma duk da haka kãmin masĩfa guda ta sãme shi, ya sãmi ni'ima biyu kõ fiye da haka.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net