Aal-i-Imraan 3:161
آل عمرانوَمَا كَانَ لِنَبِىٍّ أَن يَغُلَّ ۚ وَمَن يَغْلُلْ يَأْتِ بِمَا غَلَّ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ ثُمَّ تُوَفَّىٰ كُلُّ نَفْسٍ مَّا كَسَبَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
Kuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu.[1] Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar ¡iyama. Sa'an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba.
[1] Gulũlu shĩ ne satar wani abu daga ganimar yãƙi a gabãnin raba ta a tsakãnin mayãka. Allah Yã ce, "Yin gulũlu haram ne a kan kõwane annabi ko da waɗanda ba a halatta wa cin ganima ba, balle ga wanda aka halatta wa. Kamar yadda gulũlu yake haram a kan annabãwa haka yake haram a kan mabiyansu.".
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net