Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 3 · Aya ta 159

Aal-i-Imraan 3:159

آل عمران

فَبِمَا رَحْمَةٍ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمْ ۖ وَلَوْ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلْقَلْبِ لَٱنفَضُّوا۟ مِنْ حَوْلِكَ ۖ فَٱعْفُ عَنْهُمْ وَٱسْتَغْفِرْ لَهُمْ وَشَاوِرْهُمْ فِى ٱلْأَمْرِ ۖ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلْمُتَوَكِّلِينَ

Ma’ana

Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara[1] da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali.

[1] Annabi shi ne makomar al'amurra ga dukkan kome, amma Allah Ya lizimta masa sauƙin hali zuwa ga sahabbansa, da yin ma'ãmala da su, ma'ãmala mai kyau, da yi musu addu'a a kõwane hãli, kuma a wurin yãƙi kõ abin da ya shãfi yãƙi, Yã lizimta masa ya yi shãwara da su, kuma Ya bã shi damar yin ijtihãdi a nan, sa'an nan Ya umurce shi daya dõgara ga Allah wajen zartaswa, a kan ra'ayin da ya gani daga gare su.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Aal-i-Imraan

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net