Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 3 · Aya ta 153

Aal-i-Imraan 3:153

آل عمران

إِذْ تُصْعِدُونَ وَلَا تَلْوُۥنَ عَلَىٰٓ أَحَدٍ وَٱلرَّسُولُ يَدْعُوكُمْ فِىٓ أُخْرَىٰكُمْ فَأَثَـٰبَكُمْ غَمًّۢا بِغَمٍّ لِّكَيْلَا تَحْزَنُوا۟ عَلَىٰ مَا فَاتَكُمْ وَلَا مَآ أَصَـٰبَكُمْ ۗ وَٱللَّهُ خَبِيرٌۢ بِمَا تَعْمَلُونَ

Ma’ana

A lõkacin da kuke hawan dũtse, gudãne. Kuma ba ku karkata a kan kõwa ba, alhãli kuwa Manzon Allah nã kiran ku a cikin na ƙarshenku.[1] Sa'an nan (Allah) Ya sãkã muku da baƙin ciki a tãre da wani baƙin ciki. Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi baƙin cikin a kan abin da ya sãme ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.

[1] Bãyan da hankalinsu ya kõma gare su sai suka ga sakamakon sãɓãwa umurnin Allah, ya zama karyewar yãƙi da rashin ganĩma.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Aal-i-Imraan

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net