Aal-i-Imraan 3:122
آل عمرانإِذْ هَمَّت طَّآئِفَتَانِ مِنكُمْ أَن تَفْشَلَا وَٱللَّهُ وَلِيُّهُمَا ۗ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ ٱلْمُؤْمِنُونَ
A lõkacin da ƙungiyõyi[1] biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majiɓincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara.
[1] Banũ salimah da Banũ Hãrisa sun tãshi kõmãwa gida su bar yãƙi, a lõkacin da Abdullahi bn Ubayyi bn Salũl ya kõma da jama'arsa, Allah Ya tsare musu ĩmãninsu, ba su kõma ba. Watau yana cewa idan wani abu na masĩfa ya sãme ku, to, kun sãɓãwa Allah ne kamar yadda ya auku a Uhdu, suka sanya Annabi ya fito daga Madĩna kuma maharba suka bar wurin da aka ayyana musu. Amma kuma ai Allah Ya Taimake ku, a Badar a lõkacin da ƙarfinku bai kai haka ba, sabõda rashin saɓawarku ga umurninSa.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net