Al-Qasas 28:76
القصصإِنَّ قَـٰرُونَ كَانَ مِن قَوْمِ مُوسَىٰ فَبَغَىٰ عَلَيْهِمْ ۖ وَءَاتَيْنَـٰهُ مِنَ ٱلْكُنُوزِ مَآ إِنَّ مَفَاتِحَهُۥ لَتَنُوٓأُ بِٱلْعُصْبَةِ أُو۟لِى ٱلْقُوَّةِ إِذْ قَالَ لَهُۥ قَوْمُهُۥ لَا تَفْرَحْ ۖ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْفَرِحِينَ
Lalle ne ¡ãrũna ya kasance daga mutãnen Mũsã, sai ya fita[1] daga tsãrinsu alhãli Mun bã shi taskõkin abin da yake mabũɗansa sunã nauyi ga jama'a[2] ma'abũta ƙarfi a lõkacin da mutãnensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah bã Ya son mãsu annashuwa."
[1] Asalin baghy zãlunci, amma ga izɗilãhi, shi ne fita daga ɗã'ar shugaban Musulmi.
[2] Yawan su saba'in, an ce arba'in, kuma an ce gõma.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net