Al-Qasas 28:74
القصصوَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ
Kuma a rãnar da Yake kiran su ya ce: "Inã abõkan tarayya Ta, waɗanda kuka kasance kunã riyãwa"[1]
[1] Bãyan Allah Ya tunãtar da Musulmi rahamarSa da kaɗaita ga bãyar da ni'ima kõ hana ta da siffõfi mãsu kwaɗaitar da mũmini ga ɗã'a ga Allah da ManzonSa, daga cikin ɗã'ã akwai yin hijira wanda yake shĩ ne kan lãbãrin sũrar, sai kuma Ya tsõratar da mai bin wanin Allah ga rashin yin hijira. Duka abin da ya hana mũminai hijira idan shi abin nan ba uzuri ne na shari'a ba, to, ya zama gunki, abin bautãwa, wanin Allah. Umurnin da ya sãɓa wa umurnin Allah duka, umurnin abõkin tãrayya ne ga Allah ga wanda ya bĩ shi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net