Al-Qasas 28:57
القصصوَقَالُوٓا۟ إِن نَّتَّبِعِ ٱلْهُدَىٰ مَعَكَ نُتَخَطَّفْ مِنْ أَرْضِنَآ ۚ أَوَلَمْ نُمَكِّن لَّهُمْ حَرَمًا ءَامِنًا يُجْبَىٰٓ إِلَيْهِ ثَمَرَٰتُ كُلِّ شَىْءٍ رِّزْقًا مِّن لَّدُنَّا وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
Kuma suka ce: "Idan mun bi shiriya tãre da kai anã fizge mu[1] daga ƙasamiu." Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, anã jãwõwa zuwa gare shi, 'ya'yan itãcen kõwane iri, bisa ga azurtãwa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba.
[1] Wanda ya makkana musu Hurumi ya zama amintacce, yanã iya tsare bãwanSa kuma Yabã shi arziki a kõ'ina yake a cikin ƙasa, sabõda haka tsõron fita daga Hurumi da tsõron wuyar abinci a wurin baƙunci, bã zai hana mũmini ya yi hijira da addininsa ba zuwa wurin yardar Allah.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net