Al-Qasas 28:55
القصصوَإِذَا سَمِعُوا۟ ٱللَّغْوَ أَعْرَضُوا۟ عَنْهُ وَقَالُوا۟ لَنَآ أَعْمَـٰلُنَا وَلَكُمْ أَعْمَـٰلُكُمْ سَلَـٰمٌ عَلَيْكُمْ لَا نَبْتَغِى ٱلْجَـٰهِلِينَ
Kuma idan sun ji yãsassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, "Ayyukanmu sunã a gare mu, kuma ayyukanku sunã a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu bã mu nẽman jãhilai (da husũma)."[1]
[1] Waɗanda aka bai wa littafi a gabãnĩn Alƙur'ãni, sũ ne Yahũdu da Nasãra,waɗansu daga cikin Malamansu sun musulunta, kamar Abdullahi bn salãmi daga Yahũdu, da Nasãran Najrãna daga Nasãra, sun musulunta. Idan ba'ali ya musulunta sai a ce dukansu ke nan sun musulunta, sai wanda ya yi girman kai ya ƙigaskiya. Bã zã a kula da shi ba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net