Al-Qasas 28:45
القصصوَلَـٰكِنَّآ أَنشَأْنَا قُرُونًا فَتَطَاوَلَ عَلَيْهِمُ ٱلْعُمُرُ ۚ وَمَا كُنتَ ثَاوِيًا فِىٓ أَهْلِ مَدْيَنَ تَتْلُوا۟ عَلَيْهِمْ ءَايَـٰتِنَا وَلَـٰكِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ
Kuma amma Mũ, Mun ƙãga halittawar wasu ƙarnõni har lõkatan rãyuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutãnen Madyana, kanã karanta musu ãyõyinMu, amma Mũ Mun kasãnce mãsu aikãwa (da kai game[1] da waɗancan lãbarai).
[1] Sanin waɗannan abũbuwa duka ga Ummiyyi a wuri mai nĩsa daga wurin da abin ya auku a ciki, da kuma nĩsa daga waɗanda abin ya fi shãfuwa, ya nũna gaskiyar abin da kake da'awa. Kuma yanã natsar da zũciyarka da zũciyar waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira tãre da ku, cewa sunã cikin tsaron Allah.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net