Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 28 · Aya ta 38

Al-Qasas 28:38

القصص

وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَأُ مَا عَلِمْتُ لَكُم مِّنْ إِلَـٰهٍ غَيْرِى فَأَوْقِدْ لِى يَـٰهَـٰمَـٰنُ عَلَى ٱلطِّينِ فَٱجْعَل لِّى صَرْحًا لَّعَلِّىٓ أَطَّلِعُ إِلَىٰٓ إِلَـٰهِ مُوسَىٰ وَإِنِّى لَأَظُنُّهُۥ مِنَ ٱلْكَـٰذِبِينَ

Ma’ana

Kuma Fir'auna ya ce: "Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba, sabõda haka ka hũra mini wuta, ya Hãmãnu! a kan lãka[1] (dõmin a yi tũbali), sa'an nan ka sanya mini bẽne tsammãnĩna zan ninƙãya zuwa ga Ubangijin Mũsã kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, inã zaton sa daga maƙaryata."

[1] Fir'auna ya fãra yin gasasshen tũbali da ake cewa ajurru, aka gina masa dõgon bene, ya hau samansa, ya harba kibiya ta tafi ama, ta kõmo da jini. Saĩ ya ce: "yã kashe Ubangijin Mũsa." Bayan haka sai benen ya karye guntu uku' guntu ɗaya ya fãɗa wa sõjansa, da yawa daga cikinsu suka mutu, guntu ɗaya kuma ya fãɗa a cikin ruwa, sauran guntu ɗaya ya fãɗa wa magina, suka mutu. Kuma cewar Fir'auna, "Lalle ne nĩ, inã zuton Mũsã daga maƙaryata," ya nũna girman kansa kawai ne ya hana shi ĩmãni, ba rashin gãnewa ba, sai dai kuma sun ga kamar bãbu Tãshin Ƙiyãma.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Qasas

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net