Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 28 · Aya ta 23

Al-Qasas 28:23

القصص

وَلَمَّا وَرَدَ مَآءَ مَدْيَنَ وَجَدَ عَلَيْهِ أُمَّةً مِّنَ ٱلنَّاسِ يَسْقُونَ وَوَجَدَ مِن دُونِهِمُ ٱمْرَأَتَيْنِ تَذُودَانِ ۖ قَالَ مَا خَطْبُكُمَا ۖ قَالَتَا لَا نَسْقِى حَتَّىٰ يُصْدِرَ ٱلرِّعَآءُ ۖ وَأَبُونَا شَيْخٌ كَبِيرٌ

Ma’ana

Kuma a lõkacin da ya isa mashãyar Madyana, ya sãmi wata jam'ar mutãne sunã shãyarwa, kuma a bãyansu ya sãmi waɗansu mãtã biyu sunã kõrar (tumãkinsu). Ya ce: "Mẽne ne shã'aninku?" Suka ce, "Bã zã mu iya shãyãrwa ba sai makiyãya sun fita, kuma ubanmu tsõho[1] ne mai daraja."

[1] Sabõda girma bã ya zuwa ya shãyar da tumakinsa, sai ya sanya mu, mu 'ya'yansa, kõ da muke mãtã. Wannan ya nũna mace tanã yin aikin maza sabõda larũra. Kuma sabõda darajar ubansu ba su shiga a cikin makiyãya ba dõmin tsaron mutuncinsu don haka ake son asali mai kyau. NĩSantarsu daga maza nau'in ƙauracewa ne na sharĩ'a.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Qasas

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net