Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 28 · Aya ta 19

Al-Qasas 28:19

القصص

فَلَمَّآ أَنْ أَرَادَ أَن يَبْطِشَ بِٱلَّذِى هُوَ عَدُوٌّ لَّهُمَا قَالَ يَـٰمُوسَىٰٓ أَتُرِيدُ أَن تَقْتُلَنِى كَمَا قَتَلْتَ نَفْسًۢا بِٱلْأَمْسِ ۖ إِن تُرِيدُ إِلَّآ أَن تَكُونَ جَبَّارًا فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا تُرِيدُ أَن تَكُونَ مِنَ ٱلْمُصْلِحِينَ

Ma’ana

To, a lõkacin da Mũsã ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai nẽman ãgajin) ya ce,[1] "Ya Mũsã! Shin kanãnufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kõme fãce ka kasance mai tanƙwasawa[2] a cikin ƙasa kuma bã ka nufin ka kasance daga mãsu kyautatãwa."

[1] Ya faɗi haka zaton Mũsã zai kashe shi ne sabõda gargaɗin da ya gabãtar a gareshi, Maganar ta nũna Mũsã ya shahara da son gyãran abũbuwa dõmin islãhi, haka ne ga al'adar mutãne wanda ya tãshi yanã gyãra sai sun tuhumce shi da neman girma.
[2] Tanƙwasa ce sanya mutãne su yi abin da bã Su son yi. Kyautatãwar islãhi bã ta sãmuwa sai da tanƙwasãwa dõmin gãlibi mutãne sun fi son ɓarna a kan kyautatãwa tãre da saninsu ga cewar kyautatãwar ita ce daidai.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Qasas

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net