Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 28 · Aya ta 14

Al-Qasas 28:14

القصص

وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُۥ وَٱسْتَوَىٰٓ ءَاتَيْنَـٰهُ حُكْمًا وَعِلْمًا ۚ وَكَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ

Ma’ana

Kuma a lõkacin da ya kai ƙarfinsa, kuma ya daidaita, Mun bã shi hukunci[1] da ilmi kuma kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

[1] Wannan ya nũna, cewa Mũsã an bã shi Annabci a gabãnin ya yi hijira zuwa Madyana. Kuma yanã ƙãra ƙarfafa wannan magana abin da ke cikin ãyã ta 16 inda ya rõƙi Allah gãfara, Ya gãfarta masa, da ãyã ta l7 wadda ta nũna ya san an yi masa gãfarar har yanã neman tsari dõmin kada ya kõma yin haka a gaba. Annabãwa sunã wahami ga abin da bã wahayi ba, sa'an nan Allah Ya gyãra kuskuren, Ya tabbatar da gaskiya.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Qasas

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net