Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 27 · Aya ta 76

An-Naml 27:76

النمل

إِنَّ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانَ يَقُصُّ عَلَىٰ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ أَكْثَرَ ٱلَّذِى هُمْ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ

Ma’ana

Lalle ne wannan Alƙur'ãni[1] yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki.

[1] Idan wannan Alƙur'ani ya ƙunsã ilmin asĩrai da yake iya gaya wa Banĩ Israĩla mafi yawan abin da sũ da kansu, suke sãɓã wa jũna a kansu, tãre da shahararsu da ilmi, da yawan Annabãwan da suka wuce a cikinsu, to, ga Lãrabãwa jãhilai hiyãka ke nan. Bãbu abin da ya wajaba a gare su, sai sallamawa ga abin da yake kiran zuwa gare shi. In abin da yake faɗa ba gaskiya ba ne, dã Banĩ Isrãĩla ne farkon mãsu nũna ƙaryarsa. Ammã ba su yi ba. Sabõda haka duka gaskiya ne. Sai kõwa ya bĩ shi ya tsĩra.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Naml

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net