Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 27 · Aya ta 48

An-Naml 27:48

النمل

وَكَانَ فِى ٱلْمَدِينَةِ تِسْعَةُ رَهْطٍ يُفْسِدُونَ فِى ٱلْأَرْضِ وَلَا يُصْلِحُونَ

Ma’ana

Kuma waɗansu jama'a tara[1] sun kasance a cikin birnin, sunã yin ɓarna, kuma bã su kyautatãwa. Suka ce: "Ku yi rantsuwa da Allah, lalle zã mu kwãnan masa,[2] shi da mutãnensa sa'an nan mu ce wa waliyyinsa. 'Ba mu halarci halakar mutãnensa ba kuma mũ, haƙĩ ƙa, mãsu gaskiya ne'."

[1] Yawan mãsu ɓarnã bã ya hana gaskiya bayyana. Kuma mai mãkirci dõmin ya halakar da mai gargaɗin addinin Allah, yanã yi wa kansa sanadin halaka kawai ne. Waɗannan mutãne tara sun yi niyyar kashe Sãlihu ne, bã da sanin danginsa ba, a wurin dayake kwãna yanã salla a masallacinsa, a bãyan gari. A can Allah ya halakar da su. Wannan shĩ ne sakamakon mãkircin da suka ƙulla.
[2] Zã mu kwãnan masa, ai zãmu kwãna da niyyar kashe shi a cikin dare, a ɓõye.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Naml

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net