An-Naml 27:32
النملقَالَتْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمَلَؤُا۟ أَفْتُونِى فِىٓ أَمْرِى مَا كُنتُ قَاطِعَةً أَمْرًا حَتَّىٰ تَشْهَدُونِ
Ta ce: "Yã ku mashawarta[1]! Ku yi Mini fatawa ga al'amarĩna, ban kasance mai yanke wani al'amari ba, sai kun halarta."
[1] Allah bai keɓance hikima ga maza kawai ba har mãtã akwai mãsu hikima a cikinsu. Sai dai Musulunci yã hana shugabancin mãtã, sabõda galibinsu ãdifarsu tã rinjãyi hankalinsu, sabõda kyautata tarbiyyar yãra. Anã fahimtar cewa iya mulki shi ne rashin fallewa da ra'ayi ga shũgaba, sai a bãyan ya shãwarci mutãnensa, kamar yadda sarauniyar Saba' ta yi da Majalisarta.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net