Al-Furqaan 25:51
الفرقانوَلَوْ شِئْنَا لَبَعَثْنَا فِى كُلِّ قَرْيَةٍ نَّذِيرًا
Kuma da Mun so, haƙĩƙa dã Mun aika da mai gargaɗi[1] a ciƙin kõwace alƙarya.
[1] Dã Muna so dã Mun aika wa kõwane gari da Annabinsa mai yi musu gargaɗi, amma ba Mu so haka ba, sai Muka aika ka kai ɗaya zuwa ga dukan dũniya dõmin Mu ɗaukaka darajarka.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net