An-Noor 24:48
النوروَإِذَا دُعُوٓا۟ إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ لِيَحْكُمَ بَيْنَهُمْ إِذَا فَرِيقٌ مِّنْهُم مُّعْرِضُونَ
Kuma idan aka kirã su zuwa ga Allah da ManzonSa, dõmin Ya yi hukunci[1] a tsakãninsu, sai gã wata ƙnngiya daga gare su sunã mãsu bijirewa.
[1] Wannan yanã nũna cewa rashin yardã da hukuncin Allah kãfirci ne. Wanda ya kai ƙãra ga kõtun al'ada alhãli kuwa yanã Musulmi kuma ya halatta haka, bã da wata lalũra ba, ya zama kãfiri sai idan ya tũba. Bã ya halatta ga Musulmi su yarda da yin kõtunanal'ãda a ƙasarsu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net