Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 24 · Aya ta 39

An-Noor 24:39

النور

وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَعْمَـٰلُهُمْ كَسَرَابٍۭ بِقِيعَةٍ يَحْسَبُهُ ٱلظَّمْـَٔانُ مَآءً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَهُۥ لَمْ يَجِدْهُ شَيْـًٔا وَوَجَدَ ٱللَّهَ عِندَهُۥ فَوَفَّىٰهُ حِسَابَهُۥ ۗ وَٱللَّهُ سَرِيعُ ٱلْحِسَابِ

Ma’ana

Kuma waɗanda suka ƙãfirta ayyukansu sunã kamar ƙawalwalniyã ga faƙo, mai ƙishirwa yanã zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kõme ba, kuma ya sãmi[1] Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisãbinsa. Kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne.

[1] Ya sãmi Allah a wurin da ƙawalwalniyar take, alhãli Allah Ya gaya masa cħwa bãbu ruwa a nan, kuma Ya nũna masa hanyar da zai sãmi ruwa, idan zai bĩ ta. Sai Allah Ya cika masa hisãbinsa da cħwa, "Allah Mai saurin sakamako ne ga wanda ya sãɓa wa umurninSa," Dõmin nan da nan mai sãɓawar zai ga kuren kansa, tun daga dũniya. HisãbinAllah yanã aukuwa da sauri a kan mai sãɓã wa umurninsada gangan.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Noor

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net