Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 24 · Aya ta 2

An-Noor 24:2

النور

ٱلزَّانِيَةُ وَٱلزَّانِى فَٱجْلِدُوا۟ كُلَّ وَٰحِدٍ مِّنْهُمَا مِا۟ئَةَ جَلْدَةٍ ۖ وَلَا تَأْخُذْكُم بِهِمَا رَأْفَةٌ فِى دِينِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْـَٔاخِرِ ۖ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَآئِفَةٌ مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ

Ma’ana

Mazinãciya da mazinãci,[1] to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu.

[1] Hukuncin waɗanda ba su yi aure ba ne, amma waɗanda suka yi aure hukuncinsu a jefe su har su mutu, bãyan sharuɗɗa sun cika, kamar yadda yake ga sunna. Kuma wannan ga hakkin 'ya'ya ne, amma bãyi, hukuncinsu bũlãla hamsin kawai.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

An-Noor

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net